On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Babban Bankin Kasa ya Karbi Tsaffin Kudi Naira Bilyan 165 Zuwa Yanzu

Tsaffin Takardun kudi

Babban Bankin kasa ya ce kawo yanzu ya karbi jimillar tsaffin kudi har naira bilyan 165, tun bayan kiran da ya yiwa jama’ar kasar nan, kan su mayar da tsaffin kudin nasu bankunan ajiya.

Daraktan harkokin kudi na Babban bankin Kasa, Rasheed Adams ne ya baiyana haka a yayin taron kwamitin tsara manufofin kudi na kasa yau a Abuja.

Yace wata  daya bayan sanarwar da aka yi,  Yawan adadin tsaffin kudin da bankin ya karba  sun zarta wanda yayi tsammanin zai karba  zuwa yanzu.

Sai dai kuma ya baiyana takaicinsa  kan yadda wasu  tsirarun yan Najeriya  ke neman kara wa’adin mayar da tsaffin kudin na Naira, yana mai cewa wa’adin da bankin ya bayar na ranar  23 ga watan janairun sabuwar shekara na nan daram.