On Air Now

ZANGON SAFIYAR LAHADI

5:00am - Noon

Babban Bankin Kasa Ya Karyata Rahotannin Janye Sabbin Takardun Kudi

CBN

Babban bankin kasa ya musanta wasu rahotanni dake baiyana cewar yana duba yiyuwar janye sabbin takardun naira ‘yan 200 da 500 da kuma dubu 1 da aka sauyawa fasali daga cigaba da zagayawa a hannun jama’a.

Wata sanarwa  da kakakin bankin, Isa Abdulmumin ya fitar a ranar Lahadi, Ya baiyana rahotannin a matsayin na  shakulatin ‘bangaro  da basu  da tushe balle makama.

Sanarwar  ta baiyana cewar  sabbin takardun kudin  zasu cigaba da yin aiki  har  nan da ranar  31 ga watan Disambar  Bana, Lokacin da za’a dena  amfani da tsaffin  takardun kudin.