On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Babban Bankin Kasa Zai Fara Daure Masu Yin Li'ki Da Kudi A Wajen Buki

Babban Bankin Kasa CBN

Babban bankin kasa CBN ya gargadi masu cin zarafin Naira da su daina, ko kuma su fuskanci dauri a gidan gyaran hali.

Ta yi gargadin cewa har yanzu dokar da ta haramta  watsa takardun naira da sunan yin li’ki, musamman a wuraren taruwar jama’a nan daram

Babban bankin kasar, Ya ce Wadanda suke aikata laifin zasu iya fuskantar  daurin wata shida a gidan gyaran hali ko kuma tarar naira dubu 50

Shugabar, Sashen Ayyuka  ta bankin, Ngozi Etim,  ita  ce  tayi  wannan gargadi.

Ta ce CBN na aiki tare da jami’an  ‘yan sanda da na hukumar  EFCC da kuma hukumar kula  da harkokin mu’ammalar  kudi  ta kasa domin dakile cin zarafin naira da ake yi.