On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Babu Sunan Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan Cikin Masu Yin Takara [INEC]

SHUGABAN MAJALISAR DATTAWA DA GODSWILL

Hukumar Zabe ta kasa Mai zaman Kanta, Ta fitar da Jadawalin Sunayen Mutanen da zasu yi takara akan wasu mukamai daban-daban a yayin babban zaben kasar nan na Badi.

To sai dai a cikin jadawalin  da Hukumar ta fitar, Ba’a ga sunan Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan da kuma Tsohon Ministan Raya Yankin Naija Delta Godswil Akpabio da kuma na gwamnan jihar Ebonyi David Umahi ba.

Mutanen ukku dai sun shiga zaben fidda gwani na shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC, To sai dai kuma daga biya sunyi mi’ara koma baya akan takarar kujerar sanata, bayan kayen da suka sha a zaben fidda  gwani na shugaban kasa.

A wata hira da aka yi dashi a gidan Talabijin na kasa a daren jiya, Kwamishinan Hukumar zabe, Kuma shugaban kwamitin Yada Labaranta, festus Okoye, Yace ba za’a tursasawa hukumar wallafa sunayen Yan takarar da basu shiga  zaben  fidda  gwani na jam’iyyunsu ba.