On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Bai Kamata Najeriya Ta Fara Tunanin Cire Tallafin Man Fetur A Yanzu Ba - Dr Abdulrazak Fagge

Masanin tattalin arziki a nan kano, Dr Abdurrazak  Ibrahim Fagge ya ce  yayi  wuri Najeriya  ta fara tunanin cire  tallafin  mai a  wannan  lokaci  da kasar nan ke  fama da kalubale  na tattalin arzikin kasa.

Najeriya kasancewarta  giwar Afrika  ta bangaren tattalin arziki  ta kashe naira Tiriliyan Biyu da bilyan 91 a matsayin biyan tallafin mai tsakanin watan  janairu zuwa satumbar  bara, wanda hakan ke nuna cewar  tana kashe  sama da naira bilyan 400 a kowane  wata a matsayin biyan tallafin mai.

A hirarsa da Arewa Radiyo, Dr Ibrahim Fagge malami a  jami’ar  Yusif  Maitama Sule dake an kano, Ya bukaci a rika  hukunta  wadanda  suke yiwa  tsarin bada tallafin man zagon kasa, a maimakon yin gaggawar  janye tallafin  man  a wannan lokaci.

Bugu da kari ya  ce  mafi akasarin kasashen da suka cigaba na samar  da tsarin bada tallafin mai  ga  jama’arsu  domin  rage  radadin tsadar  rayuwa  da suke  a ciki.