On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Bakuwar Tsutsa Ta Kori Mazauna Unguwar Gayawa Gandu Daga Gidajensu A Jihar Kano

Mazauna garin Gayawa Gandu da ke karamar hukumar Ungoggo a jihar Kano bukaci daukin gaggawa daga gwamnatin jihar Kano  kan wasu tsutsotsi da suka addabi yankin, tare da tilasta musu barin gidajensu.

Wasu daga cikin mazauna garin Ibrahim Umar da Jamila Abdullahi da suka zanta da Arewa Radio, sun bayyana cewa tsutsotsin sun mamaye yankin tun a daren jiya wanda ya tilasta musu barin gidajensu.

Sai dai mazauna yankin sun kara da cewa dukkan iyalansu sun kauracewa gidajensu.

Sun kuma roki gwamnati da ta kai musu dauki domin magance tsutsotsin saboda fargabar lafiyarsu da dukiyoyi.