On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Bankin Duniya Ya Shawarci Gwamnatin Tarayya Ta Maida Farashin Litar Mai 750

BANKIN DUNIYA

Bankin Duniya ya ce har yanzu gwamnatin tarayya na iya biyan tallafin man fetur kasancewar har yanzu farashin man fetur a kasar nan bai yi tsadar data wuce makadi da rawa ba.

Babban masanin tattalin arziki na Bankin Duniya a Najeriya, Alex Sienaert,  ya  tabbatar da ci gaba da biyan tallafin man fetur da gwamnati ke yi  a Abuja, yayin gabatar da jawabinsa  a wajen  wani  taron mahangar  cigaban kasar  na  watan  Disambar da muke ciki.

Ya ce har  yanzu  farashin man fetir a kasar nan bai yi daidai  da yanayin kasuwar mai  ta duniya  ba, inda  y ace  kamata ya yi   farashin litar man  ta kai naira  750  a maimakon naira 650 da ake siyar  da ita a  halin yanzu.

 Wannan tsokaci  na zuwa ne , yayin da ‘yan Najeriya da dama suka ajiye motocinsu sakamakon  tashin gwauron zabo da suka ce  farashin  na Man  fetir ya  yi, sannan kuma aka samu   tashin kayan masarufi, biyo  bayan karin farahin man  fetir  da aka yi, wanda ke kamawa tsakanin naira  650 zuwa 700 akan kowacce  lita  daya.