On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Bankuna Sun Gudanar Da Aiki A Ranakun Karshen Mako Domin Wadata 'Yan Najeeiya Da Takardun Naira

Babban Bankin kasa CBN  ya saki  tsofaffin takardun kudi na Naira ga bankuna yayin da babban bankin ke kara zage damtse wajen farfado da tattalin arzikin kasa da karin makudan kudade bayan da aka dauki lokaci  ana fama da matsalar kudi a kasarnan.

A ranar Alhamis ne CBN ya fara sakin biliyoyin Naira ga bankunan ajiya.

Jami’an bankin sunce CBN ya sake sakin biliyoyin Naira ga bankuna a ranar Juma’a.

An bude rassan bankuna da dama a ranakun Asabar da Lahadi kuma suna bada  tsabar kudi ta Injinan ATM da kuma kan kanta.

Wasu daga cikin bankunan sun aikawa abokan huldarsu sakonnin Email suna sanar da su cewa za’a bude banki a karshen mako kamar yadda babban bankin kasa CBN  ya bada uamarni.