Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya bayyana cewa ƙudirin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na kafa 'yan sandan jihohi wani babban mataki ne na magance matsalar rashin tsaro.
Barau ya ce an tsara wannan gyara ne bayan tattaunawa mai zurfi da masu ruwa da tsaki, kuma an tanadi matakan kariya domin hana amfani da rundunar ta hanyar siyasa, tare da ƙarfafa aikin tsaron al'umma.
Ya ƙara da cewa 'yan sandan jihohi za su taimaka wa Rundunar 'Yan Sandan Najeriya wajen inganta yaƙi da laifuffuka irin su garkuwa da mutane da fashi da makami, ta hanyar amfani da jami'an tsaro da aka ɗauka aiki daga yankunan da za su yi aiki.
Comments
Add a comment