On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Barau Ya Rubuta Wasika Ga Nuhu Ribadu Kan Barazanar Kachalla Maha A Kano

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya rubuta wa Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu, game da barazanar da wani fitaccen shugaban ‘yan fashin daji, Kachalla Maha, ya yi na kai wa Jihar Kano hari.

Barazanar Kachalla, wacce ke cikin wani faifan bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta, an bayyana cewa Jihar Kano da wasu al’ummomi a Jihar Katsina su ne aka sa gaba a harin. Faifan ya kara firgita mazauna yankin tun bayan fitar sa. 

A cikin wasikar da ya sa hannu da kansa a ranar 15 ga Yuli, 2026, mai taken "Barazanar Kachalla Maha: Kira Ga Matakan Tsaro Na Rigakafi Da Aikin Tsaro Na Hadin Kai," Sanata Barau ya ce barazanar ta tayar da hankalin mazabarsa, musamman saboda kusancin al’ummomin Jihar Kano ta Arewa da Jihar Katsina.

Hakanan an kuma tattauna batun a ranar Litinin yayin ziyarar da wakilai daga Kwamitin Zaman Lafiya da Tsaro na karamar hukumar Shanono, karkashin jagorancin Farfesa M. D. Abubakar, suka kai wa Sanata Barau a Majalisar Dokoki ta Tarayya da ke Abuja.

Wani bangare na wasikar ya ce: "Na rubuto wannan wasika ne don jawo hankalin ku cikin gaggawa game da barazanar tsaro da wani fitaccen shugaban ‘yan fashi, Kachalla Maha, ya yi, inda ya yi barazanar kai wa Jihar Kano da kewayenta hari.

"Yaduwar faifan ya haifar da tashin hankali a tsakanin al'umma. Wannan lamari ya shafe ni musamman a matsayina na wakilin Jihar Kano ta Arewa, wacce ke da iyaka da wasu sassan Jihar Katsina da suka sha fama da ‘yan fashi da sauran munanan laifuka.

"A cikin mazabar, kananan hukumomin Shanono, Gwarzo, da Tsanyawa sun kasance cikin hadari musamman saboda kusancinsu da al’ummomin Jihar Katsina da ke fama da ‘yan bindiga."

Sanata Barau ya lura cewa kusan garuruwa 30 a cikin kananan hukumomin uku na cikin mafi hadari. Ya kara da cewa, ganin muhimmancin tattalin arzikin Jihar Kano ga yankin Arewa maso Yamma da kuma kasar baki daya, duk wani tabarbarewar tsaro a wadannan al’ummomi zai iya yin tasiri ga lafiyar jama’a, harkokin tattalin arziki, da kwanciyar hankalin yankin.

Ya kara da cewa: "Don haka ya zama wajibi a dauki matakan rigakafin da suka dace don hana miyagu damar aiwatar da shirinsu.

"Ina rokon ku da ku yi la’akari da inganta hadin kan leken asiri, ci gaba da karfafa sa ido, da sauran matakan da ofishin ku ke ganin ya dace don hana duk wani hari kamar yadda Kachalla Maha ya yi barazana.

"Ina kuma amfani da wannan damar don yaba wa jagorancinku wajen karfafa kokarin tsaro da leken asiri na kasar don tallafawa Manufar Renewed Hope ta Mai Girma Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR, da Babban Kwamandan Sojojin Tarayyar Najeriya. Ina da yakinin cewa ofishin ku zai ci gaba da daukar matakan da suka dace don kare rayuka da dukiyoyin Najeriya da kiyaye tsaron kasa."

Hakanan a halin yanzu, Sanata Barau ya sanar da bayar da gudunmawar babura 300 ga jami’an tsaro da ‘yan sa kai a kananan hukumomin uku da ke fuskantar barazanar ‘yan fashi a Jihar Kano ta Arewa.

Za kuma a raba kayan abinci ga wasu al’ummomin yankin.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Thundery shower

    High: 35°C | Low: 23°C