On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Barcelona Ta Lashe Gasar Laliga Yayin Da Aresenal Tasha Kashi A Hannun Brighton

A karon farko kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta lashe gasar La Liga tun bayan daga kofin a shekarar 2019, bayan da ta lallasa Espanyol da ci 4 da 2 a wasan da suka fafata a ranar Lahadi, inda ta yi fafutikar karbe kanbun gasar daga hannun Real Madrid.

Kungiyar ta  yankin  Catalonia ta lashe gasar ne  a karo  na 27, Sai dai kuma daga  bisani  wasu mutane  da  suka  yi  dirar  ba zata cikin filin wasan,sun rika korar magoya bayan kungiyar  kwallon  kafa ta  Barcelona da suke murnar lashe  gasar.

Ita kuwa kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta yi bankwana da gasar Firimiya bayan da Brighton ta  casa  ta da ci 3 da nema.

Daga karshe Manchester City  ta lallasa  Everton da ci 3 da nema.