On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Bayan Lashe Kofin Duniya Na 2022 Messi Zai Cigaba Takawa Argentina Leda - Qatar

Kasar Argentina ta lallasa Faransa da ci 4-2 a bugun daga kai sai mai tsaron raga bayan wasan karshe da suka buga da yammacin ranar Lahadi, inda Argentina ta lashe  gasar cin kofin duniya ta 2022 a Qatar.

An tashi wasan da ci 2-2 inda  bayan karin lokaci aka kammala  3-3, al’amarin da ya tilasta shiga bugun daga kai sai mai tsaron gida domin tantance wanda ya yi nasara.

‘Yan wasan Kudancin Amurka sun samu nasara ta hannun kyaftin dinsu Lionel Messi wanda ya zura kwallo a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Nasarar  ta sa Faransa ta zama kasa ta uku a bana bayan da ta lashe kofin na karshe a Rasha a shekarar 2018.

Italiya da Brazil su ne sauran kasashen biyu da suka samu nasarar a sauran matakan gasar.

Messi wanda zai cika shekaru 36 a shekara mai kamawa ya yi amannnar cewa har yanzu akwai gudummawa da zai bai wa kasarsa a fannin kwallon kafa.

Dan wasan ya ce yana jin dadin kasancewa a tawagar kwallon kafar kasarsa, kuma zai  so ya ci gaba da buga mata karin wasanni.

Messi,  wanda wannan ita ce gasar kofin duniyarsa ta 5 ya ci kwallaye 2 a wasan karshen, kana ya ci 1 a lokacin bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Shine ya ci kyautar dan wasan da ya fi yin fice a gasar, bayan da ya yi bajinta ya ci kwallaye 7.