On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Bayan Shan Rantsuwar Kama Aiki Sabon Gwamnan Jahar Osun Adeleke Ya Soke Nade-Naden Oyetola

Sabon gwamna Ademola Adeleke na jahar Osun ya sanar da nadin mukamai uku bayan rantsar da shi ranar Lahadi.

A wata sanarwa da aka fitar a Osogbo, Adeleke ya nada tsohon shugaban karamar hukumar Osogbo, Mr Kassim Akinleye, a matsayin shugaban ma’aikata.

Ya kuma amince da nadin Mr Teslim Igbalaye a matsayin sakataren gwamnatin jihar yayin da Mr Olawale Rasheed shi ne babban sakataren yada labarai.

Duk nade-naden sun fara  aiki nan take.

A baya Adeleke ya bayar da umarnin rufe dukkan asusun jihar nan take tare da soke dukkan nade-naden da magabacin sa, Adegboyega Oyetola, ya yi daga ranar 17 ga watan Yuli na shekarar  2022, har zuwa barinsa ofis.

Shi kuwa tsohon gwamnan Jahar ta Osun, Gboyega Oyetola yace ya bar Naira biliyan 14 a cikin asusun jihar duk da cewa bai ciyo bashin ko sisin kwabo ba a lokacin mulkinsa.

A sakonsa na ban kwana a ranar Lahadi, Oyetola ya ce gwamnatinsa ta biya Naira biliyan 97 daga cikin bashin da ya gada a shekarar 2018 lokacin da ya karbi mulki.

Ya ci gaba da cewa gwamnatin sa ba ta ciyo bashin kudi ga tattalin arzikin jihar ba, yana mai cewa gwamnatinsa ta dora tattalin arzikin jihar kan turba, ta hanyar ayyukan da suka  shafi jama’a da kuma mayar da hankali ga talakawa.