On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Binani Ta Kai Karar Hukumar INEC Gaban Kotu Kan Soke Ayyanata Amatsayin Zababbiyar Gwamna A Jihar Adamawa

‘Yar takarar gwamna a karkashin jam’iyyar APC, Aisha Dahiru, wacce aka fi sani da Binani, ta shigar da kara gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja domin a sake yin Nazari kan  hukuncin da hukumar zabe ta INEC ta yanke kan sakamakon zaben gwamna a jihar Adamawa.

Hakan na zuwa ne dangane da ayyanata amatsayin wadda ta lashe zaben gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris da kuma zaben cike gibi  na ranar 15 ga watan Afrilu.

Binani tana kuma neman umarni na kotun da zai  hana INEC daukar wani mataki na gaba wajen bayyana wanda ya lashe zaben har sai an tantance bukatar ta.

Da soke ayyanawar da akayi ma ta, Sanata Binani ta ce INEC ta dauki hurumin kotun sauraron kararrakin zabe wadda ita ce kotu daya tilo da ke da hurumin bada wani umarni akan zaben.

Ta gabatar da cewa kotu ce kadai za ta iya soke sanarwar jami’in INEC ba ita kanta INEC din  ba.