On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Bola Tinubu Ka Iya Dawowa Najeriya Yau Litinin Bayan Kammala Hutu A Kasashen Ketare

Muddin ba’a samu wani sauyi ba, zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu na iya dawowa Najeriya  a yau Litinin.

A ranar 21 ga watan Maris ne Tinubu ya yi balaguro zuwa birnin Paris da Landan domin ya huta da kuma tsara shirin karbar mulki gabanin rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu.

Sakataren yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, James Faleke, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, ya ce jirgin saman Tinubu tare da matarsa, Sanata Remi Tinubu, zai sauka a Abuja da karfe 2 na rana.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake takaddamar shugabanci majalisun wakilai da Dattijai, kuma ake saran Tinubu zai nuna tsarin da za’abi wajen fitar da jagorancin majalissun.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Thundery shower

    High: 37°C | Low: 23°C