On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Buba Galadima Ya Bukaci Shugaban Kasa Ya Sauke Shugaban Hukumar Zabe

Buba Galadima

Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, Ya yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya sauke shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, Farfesa Mahmood Yakubu daga kan kujerarsa, sakamakon zarginsa da kasa yin abunda ‘yan Najeriya suka yi tsammanin gani a zaben da ya gabata.

A  hirarsa  da gidan Talabijin na Channels, Ya  ce   girman lefin da  shugaban hukumar  zabe  ta  Farfesa  Mahmood  Yakubu ya aikata  ya fi  girman zunubin da dakataccen gwamnan babban bankin kasa,Godwin Emefiele ya yi.

Ana dai cigaba da sukar hukumar zaben ta kasa  kan kin dora  sakamakon zabe akan rumbun tattara  sakamakon zaben ta dake kan internet kamar yadda  ta yi  alkawari,  Koda ya ke  hukumar  ta alakanta  faruwar  matsalar  da  tangarda  ta  na’ura da aka samu.

Idan ba’a manta ba  suma tawagar  jami’an sanya ido kan zaben da aka yi kasar  nan, daga kungiyar  taraiyyar  turai, Sunce  amannar  da  jama’a  ke  da ita kan hukumar zabe ta kasa,  ta  gamu da babbar tawaya.