On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Buhari Ya Bada Takardar Daukar Aiki Ga Masu Hidimtawa Kasa 65

BUHARI

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da bada takardar daukar aiki kai tsaye ga wasu masu aikin hidimtawa kasa guda 65.

Da yake jawabi a wajen bukin cika shekara hamsin da kafa  hukumar kula da shirin masu hidimtawa kasa  a  dakin taro  na fadar shugaban kasa dake  Abuja, Shugaban kasar  ya baiyana irin dimbin nasarorin da aka samu  a sakamakon bijiro da shirin shekara hamsin da  ta gabata.

Shugaban kasar  ya baiyana cewar,  Daga cikin mutanen  da aka dauka aiki,  An  kuma karrama wasu guda  52  da lambobin karramawa, Yayin da guda  13 da  suka kasance  masu bukata ta musamman  zasu ci gajiyar shirin bada jari  dake karkashin hukumar ta NYSC.

Bugu da kari, Shugaban kasar ya baiyana  cewar , za’a  kuma baiwa  mutanen tallafin karo  karatu  domin  cigaba  da gudanar da  karatunsu a jami’ar da suka zaba cikin kasar  nan.