On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Buhari Ya Jajantawa Mutane mutum 508,721 Da Suka Gamu Da Ambaliyar Ruwa A Sassan Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa mutane 508,721 da ambaliya ruwa ta shafa a sassa daban-daban na  Najeriya.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu ya fitar, shugaban ya yi alkawarin  cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da bayar da taimakon gaggawa ga wadanda iftila'in ya shafa.

Ya kuma yi kira ga daidaikun masu hannu da shuni da kungiyoyi da su taimaka wa dubban mutanen da lamarin ya shafa.

Shugaba Buhari ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwwar gwamnatocin jihohi, za su yi aiki tare wajen rage barnar da ambaliyar ta yi.

Haka kuma sanarwar ta ambato shugaban na kira ga mazauna wuraren da ka iya fuskantar ambaliya da su rika amfani da gargadin farko da hukumomi ke yi musu game da yiyuwar afkuwar ambaliyar.

An dai samu rahotonnin ambaliya ruwa a jihohin Legas, da Yobe, da Borno, da Taraba, da Adamawa, da Edo, da Delta, da Kogi, da Niger, da jihar Plateau.

Sauran sun hadar da Benue, da Ebonyi, da Anambra, da Bauchi, da Gombe, da Kano, da Jigawa, da Zamfara, da Kebbi, da Sokoto, da Imo, da kuma jihar Abia, tare da babban birnin kasar Abuja, inda lamarin ya shafi mutum 508,721, tare kuma da raba sama da mutum 73,379 da muhallansu.

Yayin da aka samu rasa rayuka 115 , sannan kuma mutum 277 suka samu raunuka.

Sanarwar ta kumama ce gwamnati ta samu rahotonnin da ke cewa gidaje kusan da 37, 633 ne suka zube sakamakon ambaliyar.