On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Buhari Ya Koka Kan Karuwar Makamai A Yankin Tabkin Chadi

shugaban kasa Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiyana cewa makaman da ake amfani dasu a yakin da ake gwabzawa tsakanin kasar Rasha da kuma Ukrain, sun fara kwarorowa yankin kasashen Afrika, musamman ma yankin tafkin Cadi.

Shugaban kasar ya baiyana haka ne a yayin taron shugabannin  kasashen yankin Tafkin Chadi karo na 16 a Abuja.

Buhari wanda shine shugaban taron, Lamarin wanda  ya kara  ta’azzara  karuwar   bazuwar kanana da kuma manyan makamai, na bukatar sake  inganta matsaron da ake dasu akan iyakokin kasashen.

Ya kara da cewa  yakin Kasashen Rasha da Ukrai, da sauran wasu kasashen dake fama da rikici a yankin Sahel na yammacin Afrika, ya kara temakawa  kungiyar Mayakan Boko Haram wajen samun wurin zama  a yankin tafkin Chadi.