On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Buhari Ya Nada Sharada Amatsayin Shugaban Wata Sabuwar Hukuma

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Sha’aban Ibrahim Sharada a matsayin babban sakataren zartaswa na hukumar kula da Almajiri da ilimin yaran da ba sa zuwa makaranta.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar, ta ce Buhari ya nada Sharada, dan majalisar wakilai mai barin gado daga Kano, bayan ya sanya hannu kan dokar kafa hukumar.

Sharada ya yi digirinsa na farko a bangaren aikin jarida daga  Jami’ar Bayero ta Kano, sannan kuma ya yi digiri na biyu a fannin harkokin kasuwanci daga Jami’ar Chichester, ta kasar Ingila.