On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Buhari Ya Saka Hannu kan Kunshin kasafin kudin 2023

Shugaban kasa Buhari Yana saka hannu kan kasafin kudin 2023

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saka hannu kan kasafin kudin bana wanda ya kai naira tiriliyan 21 da bilyan 83 da kuma kwarya-kwaryar kasafin kudin shekarar data gabata.

A lokacin da yake saka hannun kan  kasafin kudin, Shugaban kasa Buhari ya baiyana cewa an  yiwa  kunshin kasafin kudin  karin  naira  tiriliyan  1 da bilyan  32, akan ainihin alkaluman kasafin kudin na  farko  da  bangaren zartawa  ya  gabatarwa majalisar dokoki  ta kasa, wanda ya kama naira  tiriliyan 20 da bilyan 51.

Dangane da kwarya-kwaryar kasafin kudin shekarar data gabata kuwa, Shugaban kasar, ya baiyana cewa , amincewa dashi zai baiwa  gwamnatinsa  damar   daukar matakan da suka dace  na yin gyararrarki akan barnar da aka samu sakamakon ambaliyar ruwa  data afkawa  bangaren aikin gona.

Ya kara da cewa, ministar kudi kasafi da kuma tsare-tsaren cigaban kasa zata yi cikakken bayani akan kunshin kasafin kudin, wanda zai yi aiki tare da tallafin dokar kudi ta shekarar   2022.