On Air Now

Off Air

Noon - 6:00pm

Buhari Ya Tafi Landan

BUHARI

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tashi daga filin jirgin saman Azikiwe dake Abuja domin halartar bikin nadin sarautar Sarki Charles na uku da aka shirya yi a karshen makon nan.

Gabanin nadin sarautar, sakatariyar Kungiyar kasashe  renon Ingila  za ta yi amfani da damar taron shugabannin da za a yi a birnin Landan domin karbar bakuncin taron koli na shugabannin gwamnatocin kasashe mambobin kungiyar a ranar Juma'a 5 ga watan Mayun da  muke  ciki.

Shugaban  kasar  ya  yi  balaguro  ne  tare  da Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha  da  Ministan Harkokin kasashen  Waje, Geoffrey Onyeama  sai   Ministan Yada Labarai da  raya  Al’adu Lai Mohammed da mai ba Shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro   Babagana Monguno.

Sauran sun hada da Shugaban  hukumar leken asiri ta kasa, Ambasada Rufai Abubakar da  shugabar hukumar  kula da  ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje,  Uwargida Abike Dabiri-Erewa, da sauran manyan jami’an gwamnati.