On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Buhari Zai Tafi Kasar Kori Ta Kudu Taron Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi balaguro daga Abuja babban birnin tarayyar Najeriya zuwa kasar Koriya ta Kudu domin halartar wani taron duniya kan harkokin lafiya da hallitu na shekarar 2022.

Taron wanda Koriya ta Kudu tare da hadin gwiwar hukumar Lafiya ta duniya suka shirya, na kwanaki biyu zai gudana tsakanin ranakun 25 zuwa 26 ga watan Oktoba.

Taken taron dai shi ne 'Makomar Rigakafi da Lafiya'

Sanarwar da Fadar Shugabancin kasar ta fitar ranar Asabar ta hannun Mallam Garba Shehu, ta ce Najeriya tare da wasu kasashen Afirka biyar ne za su halarci taron, wanda za a ba da horo kan yadda za a dinga samar da rigakafin cutuka bisa fasahar MRNA ga nahiyar Afirka.

Shugaba Buhari, wanda ake sa ran zai gabatar da jawabi a wajen taron, zaiyi kuma ganawa daban-daban da shugaban kasar Koriaa ta Kudu  domin tattauna wasu hanyoyin hadin gwiwa  da ke tasiri ga rayuwa da lafiyar 'yan Najeriya.

Daga cikin wadanda za su yiwa shugaba Buhari rakiya zuwa Koriya ta Kudu, akwai ministan lafiya Osagie Ehanire, shugabar hukumar NAFDAC, Farfesa Mojisola Christianah Adeyeye da shugaban hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta NCDC, Dakta Ifedayo Adetifa.

Sauran sun hada da wasu gwamnoni, ministoci da kuma wasu manyan mukarraban gwamnati.

Sanarwar fadar shugabancin kasar ta ce, ana sa ran shugaba Buhari zai koma gida da zarar an kammala taron.

Karin Magana:    Bakar Masara ba gashin Yaro ba.

More from Labarai