On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Buhari Zai yi Balaguro Zuwa Portugal A Ziyarar Kwana Hudu.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai yi balaguro zuwa Portugal a ziyarar kwana hudu.

A wata sanarwa da mai Magana da yawunsa, Mallam Garba Shehu, ya fitar, ya ce shugaban zai gana da takwaransa na Portugal, Shugaba Marcelo Rebelo, sannan kuma za a karrama shi da lambar girmamawa da kuma ta Masarautar kasar a ziyarar.

Hakan na zuwa ne kwana biyu bayan dawowarsa daga taron koli na shugabannin kungiyar Commonwealth a Kigali babban birnin Rwanda.

Ana sa rana shugabannin biyu za su jagoranci wani babban taron tattaunawa da kulla yarjeniyoyi na kasashen biyu, sannan kuma su sanyo hannu a kan abubuwan da suka amince a tsakaninsu.

Shugaban na Najeriya zai kuma ziyarci majalisar dokokin kasar ta Portugal inda zai tattauna da shugabanta Dakta Augusto Santo Silva, da kuma Firaministan Portugal din, Antonio Costa

Haka kuma Shugaba Buhari zai gabatar da jawabi ga gamayyar 'yan kasuwa na Najeriya da Portugal, kana daga bisani ya yi tattaunawa ta musamman da wasu zababbun 'yan kasuwar na Portugal masu zuba jari.

Har Ila yau Buhari zai halarci taron Majalisar Dinkin Duniya da ake yi a kan tekunan duniya, taron da aka fara ranar jiya Litinin a Lisbon, wanda kuma za a kammala ranar 1 ga watan Yuli

Wadanda za su yiwa shugaban rakiya sun hada da Ministan Harkokin Waje Geoffrey Onyeama da Ministan Yada Labarai da Al'adu, Lai Mohammed da Ministan Masana'antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Adeniyi Adebayo.

Sauran sun hada da Ministan Matasa da Wasanni, Sunday Dare da Ministan Sadarwa da Tattalin Arzkin Harkokin Intanet, Isa Pantami, na daga cikin masu rufa wa shugaban baya.

Za su dawo gida Najeriya  ranar Asabar 2 ga watan Yuli, kamar yadda sanarwar ta bayyana.