On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Burtaniya Zata Shiga Jerin Manyan Kasashe Mafi Tabarbarewar Tattalin Arziki A Bana

IMF

Burtaniya na shirin zama daya daga cikin manyan kasashe mafi tabarbarewar tattalin arziki a bana, a cewar bada asusun lamuni na duniya IMF.

Asusun ya baiyana cewar  tattalin arzikin Birtaniya a shekarar 2023 zai kasance mafi muni a cikin manyan kasashe 20 masu karfin tattalin arziki, da aka fi sani da G20, wanda ya hada da  kasar  Rasha da  aka kakabawa takunkumi.

Asusun na IMF ya yi hasashen tattalin arzikin Burtaniya zai ragu a wannan shekara.

Hakan ya biyo bayan faduwar wasu bankunan Amurka guda biyu a watan da ya gabata, bayan da Bankin  UBS da suke  gogagga  dashi  ya yi gaggawar kwace babban bankin kasar Switzerland , lamarin da ya kara  haifarwa  kasar  ta burtaniya dagulewar  lamura.