On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Burutai Ya Barranta Kansa Da Wasu Kadarori Da Hukumar ICPC Ta Kwace A Abuja.

Tsohon Babban hafsan Sojan kasar nan, Laftanar janar Tukur Burutai, Ya nesanta kansa daga wasu kadarori cikinsu hadda wasu kudade kimanin naira bilyan 1 da Milyan 800 da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Kuma Karbar Rashawa ta kasa ICPC ta kwace a Abuja.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar  14 ga watan jiya, tace jami’anta sun kai sumame wani gida dake yankin Wuse 2, mallakin kanfanin K salam Construction Company.

Jim kadan bayan sumamen ne, wasu rahotanni suka baiyana cewa kadarorin mallakin tsohon babban hafsan sojin kasar nan Laftanar Janar Tukur Burutai, Inda jam’iyyar PDP ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaggauta yiwa jakadan kiranye.

To sai dai kuma a yayin wani taron manema Labarai da Lauyansa Ugochukwu Osuagwu yayi, Ya baiyana rahotannin da ake danganta kadaraorin da Buraitai a matsayin na rashin gaskiya.