On Air Now

ZANGON MARAICEN LAHADI

6:00pm - Midnight

CHANJIN KUDI: Buhari Zai Yiwa 'Yan Najeriya Bayani Ranar Alhamis

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi jawabi ga 'yan kasa a yau Alhamis 16 ga Fabrairu, 2023 da karfe 7 na safe.

Mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da hulda da  Jama'a, Femi Adesina shine ya tabbatar da hakan ya cikin Wata sanarwa da ya fita a cikin daren da ya gabata.

Sanarwar ta umurci gidajen Talabijin da gidajen Rediyo da sauran kafafen yada labarai na zamani da su kasance da gidan Talabijin  na kasa NTA da kuma  gidan Rediyon tarayya domin  shugaban kasar.

A kasance da tashar Arewa Radio mita 93.1FM ko ta  Internet akan www.arewaradio.com daga ko'ida a duniya domin jin jawabin na shugaba Buhari ga 'yan Najeriya.