On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Chief Gabriel Aduku Ya Zama Sabon Shugaban Kungiyar Tuntuba Ta Arewa

Tsohon ministan lafiya a zamanin gwamnatin Goodluck Jonathan, Chief Gabriel Aduku ya zama sabon shugaban kungiyar tuntuba ta Arewacin kasar nan.

Sakataren kungiyar , Burka Zarma  ne ya sanar da haka, yayin wani taron manema labarai a jiya, jim kadan bayan kammala wani zaman kolin kungiyar,  wadda  ta amince da Aduk a matsayin sabon shugaban ta.

Chief Gabriel Aduku   ya karbi ragamar  shugabancin kungiyar tuntuba  ta Arewa daga hannun  tsohon ministan aikin Gona, Chief Audu Ogbeh, wanda  wa’adin shugabancinsa  ya kare a watan Maris.

Zai rike  shugabancin jam’iyyar  nan da tsawon shekara  ukku mai zuwa.