On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Cikin Hawaye 'Dan Takarar Mataimakin Shugaban Kasa Datti Baba-Ahmed Ya Bayyana Damuwa Kan Yadda Ake Zargin Iyalansa Saboda Yana Yiwa Obi Mataimaki

‘Dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar Labour, Datti Baba-Ahmed, ya zubar da hawaye a daren ranar Lahadi da ya gabata, a yayin wani taron tattaunawa da gidan talabijin na Channels ya shirya.

Baba-Ahmed, wanda ke magana kaitsaye tare da Peter Obi, dan takarar shugaban kasa, yace iyalinsa sun zama ababen muzantawa da zagi bayan an zabe shi a matsayin abokin takarar Obi.

Yayin da ya ke furta wadannan kalamai, dan takarar mataimakin shugaban kasar ya yi kokarin zure karayar zuciya da hawaye kafin wani lokaci ya bada  uzuri ya fice daga zauren.

Masanin tattalin arzikin ya bayyana cewa zai fi farin ciki sosai idan masu sukarsa suka tsaya akansa  shi kadai.

More from Labarai