On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Cin Hanci Da Tarin Kura-Kurai Sun Dabaibaye Shirin Asusun Kula Da Lafiya Kyauta Na Gwamnatin Taraiyya ( BHCPF) A Jihar Kano

MOTAR DAUKAR ITACE DA TA KOMA DAUKAR MARASSA LAFIYA

Wata tsohuwar Akori Kura da ake 'daukar itace da ita, ta koma motar daukar marassala lafiya wuta ta juya motar daukar marasa lafiya domin ceto mata masu rayukan mata masu juna biyu, Sannan Kuma an sayi wani kwandon zuba shara a kan Naira Dubu 100. “A wasu asibitocin, shugabanninsu nada ikon cire kiman Naira miliyan biyu, yayin da ka’idar ta ce ba za su iya fitar da fiye da naira dubu Hamsin ba, wasu kuwa na ikirarin cewa sun yiwa wadansu dakunan asibitocin fenti, Amma magana ta gaskiya ba'a yi wannan fentin a hukumance ba.

Mai Rahoto Kolawole Omoniyi.

 

 

TSOHUWAR MOTAR DAUKAR ITACE WADA TA KOMA MOTAR DAUKAR MARASSA  LAFIYA

wannan  Tsohuwar motar daukar kayan mai launin rawaya, an Samar da ita ne domin jigilar kaya masu nauyi , musamman  itacen yin girki  daga wani kauyen zuwa wani a kewayen garin Jeli dake karamar hukumar Tudunwada ta nan jihar Kano.

To sai dai wani hanzari ba gudu ba, Da zarar Dare ya kawo jiki, tsohuwar motar guda daya da ake amfani da ita a garin  mai tazarar kilomita 120 daga birnin Kano a kodayaushe a shirye take domin ceto duk wani mara lafiya saboda rashin ingantaccen Asibiti da rashin kyawun hanyar da zata kaika kauyen.

Duk da kasancewar motar ba ta da cikakkiyar lafiya da kuma rashin kyawun Yanayi ga marassaa lafiya, mai motar, Haruna Sani, Dan  shekaru 45 a duniya, ya ce ya yi amfani da motar wajen ceto rayukan mutane  sama da  80 , Wanda akasarinsu   mata masu juna biyu ne,  a garin a  shekaru 15 da suka gabata.

Tsohuwar motar ta zamarwa mutanen yankin motar daukar marassa lafiya a duk lokacin da wani Abu na Neman agajin gaggawa ya taso, duk da kasancewar ta siradi tsakanin mutuwa da rayuwa.

WATA MATA MAI CIKI WADDA TAYI RASHIN SA'A TA MUTU A CIKIN MOTAR BAYAN WATA DOGUWAR NAKUDA DATA FUSKANTA.

Wata Mata Mai Ciki wadda tayi rashin sa'a ta mutu a cikin motar bayan wata doguwar Nakuda data fuskanta.Duk da cewar  malam Sani  yana kokarin tallafawa jama’a ne, To sai  dai  Hassana Ibrahim ba ta  yi sa’ar  samun  haka ba, Duk da cewar an kwantar da ita cikin tsohuwar motar domin kaita Asibiti, To  sai dai kuma motar ta samu matsala ta bangaren makunninta.

Duk da cewar  an hada tawagar wasu  manyan mutane domin tura motar har tsawon mintuna 30. Daga nan aka fara tafiyar sama da kilomita 20 zuwa asibiti mafi kusa. Sai dai kash Hassana ta rasu a hanya ba da jimawa ba.

Bayan haka ne ,  Motar  ta fara  yin tafiya wadda za’a  shafe  tsawon sama da Kilomita  20 kafin a kaiga zuwa  Asibitin, Sai dai kuma abun  alhinin  Hassana  ta riga mu gidan gaskiya akan hanyar kaita asibitin.

‘’ Watakila  da Hassana  ba zata mutu ba, Da ace motar  tawa tana da cikakkiyar  koshin lafiya’’ A cewar Sani.

‘’Tana fama da nakuda a cikin motar da aka kwantar da ita, wadda  muka  fara  turawa  tsawon  mintina  30, har ta kaiga karfinta ya ‘kare, yayin daga bisani kuma ta ce ga garinku nan, a lokacin da muke gab da ‘karasawa Asibitin.

MALAM SANI DIREBEN MOTAR

Asibitin Sha Ka Tafi  na garin Jeli, Na da tazarar kilomita  100 daga gidansu marigayi ya  Hassana, Sai dai kuma bashi da isassun kayan kiwon lafiya da ake bukata domin sakara mai juna biyu. Wannan shine dalilin da yasa aka dauki Hassana zuwa wani asibitin mai tazarar kilomita  20 kafin ta gamu da ajalinta.

ASIBITIN GARIN JELI

TAKADDAMA AKAN  WANDA YA KAMATA YACI GAJIYAR SHIRIN BHCPF , YA KAWO KATSALANDAN WAJEN AIWATAR DA SHIRIN A ASIBITIN JELI

 

Asibitin  Jeli na cigaba da kasancewa a yanayi na ban takaici  duk kuwa da kasancewar daya daga cikin masu cin gajiyar  hirin Asusun Kula Da Lafiya Kyauta Na Gwamnatin Taraiyya   [BHCPF]. Shekaru biyu bayan Kano a matsayin na jiha ta fara aiwatar da shirin, Sai dai kuma babu wani tasiri da shirin ya haifar ga Asibitin.

Ga dalilin da suka haddasa samun hakan,  Daga cikin  masu ruwa da tsaki na Asibiyin Jeli da Yaryasa dake a  mazabar  Yaryasa  ta karamar hukumar Tudunwada, ana ta takaddama  kan wanda ya da ikon cin gajiyar shirin na  BHCPF.

Wani Ma’aikacin Hukumar  kula da shirin Temake-keniyar Lafiya na jihar Kano, Akarami Nuhu Aliyu, (KSCHMA) dake Asibitin  Yaryasa , ya yi ikirarin cewa yana cikin wadanda aka horas domin gudanar da shirin a Asibitin  Yaryasa kafin a karkatar dashi daga Asibitin.

A cewarsa, an karkatar da shirin ne saboda rashin warware takaddamar da ke tsakanin tsohon shugaban Asibiyin Yaryasa, Magaji Ubale, da kuma   tsohon shugaban shugaban sashensa,  Suraju Sabayuki.Dukkanin mutanen da zasu ci gajiyar shirin yan asalin garin Yaryasa ne, Amma saboda karkatar dashi da aka yi, Jami’an Asibiyin Jeli ne kadai ke da ikon yin ta’ummuli da kudin gudanar da shirin dake cikin Banki.

" Garin Jeli yana da nisan sama da kilomita 20 daga  Garin  Yaryasa, Sai dai wadanda suke a cikin shirin  ba za su  iya biyan kudin abun  abun hawa daga kauyen garin nasu ba, wanda  ya kama naira 800, sai kuma  tarnakin aiwatar da shirin a dukkanin   asibitocin biyu’’ kamar yadda  Aliyu  ya baiyana.

Kazalikaza  Wani  dattijo mai bukata ta musamman dan shekaru 65 a duniya, Shehu Garba, da kuma Babban Limamin  garin Yaryasa Iliya  Saleh  Dan shekaru  80  a duniya, na daga cikin wadanda suka yi rajistar cin gajiyar shirin . Sun koka da cewa duk wani fatansu na  samun kula da  lafiya kyauta a Asibitin  Garin  Yaryasa ya gamu  tazgaro  sakamakon  an karkatar da shirin.

Malam Shehu Garba Da Iliya Saleh

Koda aka   tuntube su ta wayar tarho, Ubale da Sabayuki sun musanta cewa suna da wani takun sa’ka a tsakaninsu. Ubala ya danganta rashin aiwatar da shirin   bisa   zargin karkatar dashi da  tsohon shugabansa yayi, Sai dai kuma  Sabayuki ya jaddada cewa  matakin da aka dauka ya samu amincewar dukkanin masu ruwa da tsaki.

Kokarin da wakilinmu ya yi na samun  karin haske kan wannan zargi, Hakan ta sa shi kai  ziyarar ba  zata  zuwa  garin na Jeli, wanda ake shan wahala kafin a isa garin wanda  mutuwar  marigayiya Hassana ta faru.

Hanyar  zuwa garin Jeli a Lalace  take, Yin Tuki a kanta abune mai  wahalar gske. Aikin gina gadar dake kan hanyar garin ya kara dagula lalacewar  ta.

A lokacin da wakilinmu ya isa wani bangare na hanyar, Dole  tasa  ya ajiye motarsa a gefen hanya, Sannan ya  hau ‘Dan Acaba  domin cigaba da tafiya.

LALACEWAR DA HANAYR GARIN JELI TA YI

Daga karshe dai ya samu nasarar ganawa  Sale Haruna, wanda ya kasance  shugaban Asibitin Jali, Wanda kuma shine kadai  cikakken ma’aikaci a Asibitin.

Tun a watan Maris na shekarar  2020 da aka nemi da ya karbe ikon tafiyar da shirin, Saia i kuma  Haruna bai iya ba da jerin sunayen wadanda suka yi rajista a karkashin shirin  a Asibitin na  Jeli ba lokacin da wakilinmu ya ziyarce shi a ranar 7 ga watan  Yulin 2022.

‘’Hukumar  Kula da Kananan Asibitoci ta jihar Kano ta ce Asibitin Jeli ne aka tantance domin cin gajiyar tsarin, wanda kuma suka sani,  na samu  kira ne kawai daga shugabanmu na wancan lokacin (Sabayuki) a tsakanin cikin watan  Maris na  2020, kan cewar a hali yanzu  za’a rika aiwatar da shirin na  BHCPF a Asibitin na  Jeli PHC.

‘’ Darakta  daga  KASHMA,[ Dr Abdullahi ] A watan yunin 2022  ya kirani kan cewar  tawagar jami’ansu zasu zo domin warware matsalar bada jimawa ba’’ kamar yada ya baiyana.

BAYANIN ASUSUN BANKI KAN GUDANAR DA SHIRIN BHCF A ASIBITIN JELI

Watanni bayan alkawarin da hukumar KASHMAS ta yiwa Haruna domin sabunta bayaann wadanda zasu ci gajiyar shirin a Asibitin na Jeli, Wakilin namu ya tuntubi shugaban ta wayar tarho  a ranar  9 ga watan Augustan 2022. Amma yace  babu  wani  da  ya ji daga hukumar.

BUGU DA ‘KARI, WATA MATA MAI SHAYARWA TA RASU  AKAN BABUR A GARIN NA  JELI

Haruna ya tabbatar da rasuwar wata mata mai shayarwa mai suna Amina Salihu. Shugaban Asibitin  ya ce ya tura Amina dake fama da karancin jini -zuwa wani asibiti mai inganci da ke Tudunwada, amma ta mutu a kan babur a kan hanyarta ta zuwa asibitin.

Da aka tuntubi Daraktan kula da shirin a Huumar ta  KASCHIMA, Dt. Abdullahi Sahad Ahmed, ya bayyana cewa, an mayar da shirin ne  zuwa Asibitin  Jeli ne  kasancewar  Asibitin Yaryasa  yana da makamancin wannan tsari a cikinsa  ga ma’aikatan gwamnati da kuma wani na marasa galihu, yayin da Asibitin  Jeli babu mutum da yake amfana da irin wannan tsari.

AN BAR JIHAR KANO A  BAYA, SHEKARU UKKU BAYAN KARBAR KASONTA NA SHIRIN ASUSUN KULA DA LAFIYA KYAUTA NA GWAMNATIN TARAIYYA  ( BHCPF)

An fara aiwatar da cikakken shirin ne a shekarar  2019, wanda a matakin farko gwamnatin taraiyya ta raba naira bilyan 6 da milyan 500 ga jihohi 15, inda jihar Kano ta samu naira milyan 948.

Duk da wannan makudan kudi da kuma kaso na biyu da aka saki a shekarar  2022, Shirin bai haifar da wani Da mai ido ba, a mafi akasarin asibitoci 881  dake cin gajiyar shirina  ziyar gani da ido da aka kai wuraren.

Masu ruwa da tsaki  sun danganta matsalar da ake samu  da  Cin Hanci  da Almubazzaranci  da kuma nuna Sakaci wajen  gudanar da aiki da sauransu.

MUTUWA, DA CAKUDA SUNAYEN  WADANDA ZASU AMFANA DA SHIRIN  YA KAWO TAZGARO WAJEN  AIWATAR DA  SHIRIN  NA  BHCPF A ASIBITOCI DA DAMA.

Ga misali, a asibitin Tsohon-Gari da ke karamar hukumar Tudunwada, an hana Mutan i 298 da ke Mazabar  Tsohon-Gari cin gajiyar shirin na  BHCPF a cikin shekaru biyu da suka wuce bayan rasuwar shugaba na Biyu mai kula da gudanar da shirin, wanda aka fi sani da 2-IC mai suna , Sani Salisu.

Umar Abdu, wanda ya kasance   Shugaban Asibitin, ya ce Salisu, wanda yana daya daga cikin wadanda suka sanya hannu kan asusun shirin kiwon lafiya kyauta na gwamnatin taraiyya  BHCPF, ya rasu  a ranar 14 ga watan  Octoban 2020. Ya yi ikirarin cewa ya rubuta wa  Hukumar kula da Asibitoci ta jihar kano KPHCMB wasika tun a cikin  Satumbar 2021 tare da e takardar dake  tabbatar da  mutuwar marigayi  Salis, domin a maye sunansa  da wani, Amma shuru ka ke ji  babu wani labara.

Matsalar da ke faruwa a Asibitin Tsohon-Gari  ta  yi  daidai da wadda  Asibtin Middle Road  dake  karamar hukumar Fagge ke fuskanta,  inda shugaban kwamitin cigaban unguwar  Alh. Yau Muhammed  ya rasu  watanni shida da suka gabata, wanda  hakan yayi sanadin yin cikas a bangaren gudanar da shirin.

Hauwa Umar Fagge wadda ta kasance  shugabar Asibitin, ta ce  daga  baya  ta yi nasarar maye gurbin sunan Muhammed da sabon shugaban kwamitin mazabar Anthony Monday - watanni biyu da suka gabata. Sai dai kuma, duk da haka, ba’a fara gudanar da cikakken   shirin na BHCPF sakamakon rashin samun izinni daga Hukumar  KPHCMB da kuma tarin kura-kuran dake cikin rijistar masu cin gajiyar shirin.

 “Babu lambar waya a kashin farko na sunayen da suka ba mu. Sannan kuma abu ne mai wahalar gaske  sake bibiyar wadanda suka yi rijista da shirin.  Sun canza mana jerin sunayen ne a makon farko na watan  Yulin  2022 lokacin da muka gano cewa mutane 27 ne kawai cikin 68 da ke cikin jerin sunayen suka kasance yan asalin wannan  Unguwa, sauran 41 kuma sun fito ne  Sabongari Gabas ne”  A cewar ta.

Kazalika Asibitin Abasawa da ke Mazabar  Tsamiya Babba a karamar hukumar Gezawa yana da masu rajistar  cin gajiyar shirin  biyu ne  kacal.  Shugaban Asibitin  Kabiru Yahaya, ya ce ba’a taba samun mutanen ba a lokacin da aka neme su.

“Muna da  wadataccen Magani  sai dai kawai sun bamu sunayen mutane biyu da ba’a san inda suke ba’’ A cewarsa.

SUNAYEN MASU CIN GAJIYAR SHIRIN A ASIBITIN ABASAWA

Hakazalika, akasarin wadanda suka yi rajista a karkashin shirin a Asibitin  Jaba  sun fito ne daga karamar hukumar Minjibir, mai tazarar kilomita 60 daga nan  Kano, kamar yadda wasu masu amfana da shirin daga Gandun Albasa da ke cikin birnin Kano suka shiga jerin sunayen wadanda zasu amfana da shirin a Asibitin  Yaryasa  dake a karamar hukumar Tudunwada.

Jihar Kano ta samu masu cin gajiyar shirin dubu 79 a kashin farko na shirin  asusun kula kiwon lafiya kyauta na gwamnatin taraiyya a nan kano  BHCPF. Sai dai kuma wakilinmu ya fahimci  cewa  anyi amfani da Alfarma wajen shigar da sunayen

Misali, shida daga cikin Asibitoci  381 masu amfana da shirin  sun sami mutum daya kadai ne daga wajensu, sannan kuma  Asibitoci 29 suna da kasa da mutane 10 kowannensu  a jerin sunayen, kamar  yadda  bayanan da Hukumar  KSCHMA ta fitar suka nuna.

HUKUMAR KASCHMA TA ZARGI MASU UNGUWANNI DA SHUGABANNIN KWAMITIN UNGUWANNI DA YIN COGE A CIKIN TSARIN.

Da take mayar da martani, Hukumar  KASCHMA, Wadda ita ce keda  alhakin aiwatar da shirin  Insorar Lafiya  na kasa  NHIS  da  kuma shirin na  BHCPF, ta danganta matsalolin da aka samu  a cikin shirin, da yin rijista har sau biyu , sakamakon dogaro da shugabannin al’umma, wadanda suka yi zargin  sun yiwa shirin  ungulu da kan zabo.

Da yake jawabi a madadin Babbar Sakatariyar Hukumar, Halima Muhammad Mijinyawa, Daraktan kula da  shirin Dr. Abdullahi Sahad Ahmed Ya ce an sake  fitar sunayen wadanda zasu ci gajiyar shirin sannan kuma aka karkatar  da sunayen.

“Mun dauka cewar  Masu Unguwanni da Shugabannin Kwamitin Unguwannci sun san mutanensu sosai, A saboda  haka muka ba su damar tantace sunayen amma yawancinsu sun sanya sunayen mutanen da suka sani ne kawai  ba tare da la’akari da wurin da suke ba,  Misali, mun gano cewa daya daga cikin wadanda suka amfana da shirin  Jami’in tsaro ne  na  Civil Defence  wanda bai cancanta ace yana cikin shirin ba,”  a cewarsa.

 

Dr. Ahmed ya ce a yanzu haka hukumar na gudanar da tantancewa a wuraren domin tabbatar da cewa duk wanda zai  gajiyar shirin ya mika lambar shaidarsa ta zama dan  kasa (NIN) kafin su ci gaba da cin gajiyar shirin.

FITAR DA CAKIN NAIRA DUBU 100 A HUKUMANCE DOMIN SIYEN KWANDON SHARA YASA AN BADA CIN HANCIN DUBU 65.

An kuma gano wata cuwa-cuwa  da aka yi a Asibitin  Jaba  inda  shugabar  Asibitin  Samira Ibrahim Ayuba, ta fitar da cakin kudi guda  bakwai domin  cire kudi daga asusun  BHCPF a cikin kwana daya. A

Ta ce cakin kudade - wanda aka fitar  a ranar karshe ta shekarar 2021 - an yi haka ne  domin  siyan wasu kayan aiki da  magunguna da biyan kudin ma'aikata na wucin gadi.

Samira ta ce an fada mata cewar  dole ne  duk wasu kudaden da ba a yi amfani dasu ba dake cikin asusun  bayan  watan Disambar 2021, A saboda haka aka yi gaggawar cire  kudin a cikin  sa'o'i 11. Amma bayan ta fahimci cewar akwai  matsaloli, ta umurci dukkanin wadanda suka amfana da shirin su dawo a kudaden.

Daya daga cikin wadanda ake zargin ta cire kudi, ta bayar da cakin Naira 100  domin siyan kwandon shara guda daya. Daga baya ta je kasuwa, ta sayi kwandon sharar a kan Naira dubu  35-000, sannan ta nemi a ba ta Naira  dubu 65 daga hannun mai siyarwar, Kabiru Ibrahim.

 

kwandon shara da Samira ta sayo

 

“Na je kasuwar Sabongari na sayi kwandon shara, sai na ce wa mai siyarwar (Ibrahim) ya karbi kudinsa  dubu 35 ya ba ni ragowar kudin  Dubu  650 a tsabarsu ,”  kamar yadda  ta baiyana.

“Daga baya aka ce min yin  hakan  ba daidai ba ne. Na koma wurinsa, na ba shi Lambar asusun BHCPF domin  ya taimaka ya saka naira dubu  70, Bayan haka, na biya shi sauran kudinsa naira Dubu 5  daga Albashi nan a naira Dubu 50 da nake  karba.

 

LITTAFIN CAKIN KUDI NA BANKI YA KAWO TSAIKO WAJEN AIWATAR DA  SHIRIN ASUSUN KIWON LAFIYA KYAUTA NA GWAMNATIN TARAIYYA   BHCPF A KANAN HUKUMOMI  6 NA JIHAR KANO.

Dukkanin Asibitoci  51 da ke a karkashin shirin na  BHCPF a cikin kananan hukumomin shida na jihar kano, da suka hada da Tsanyawa, Bichi, Kunchi, Garko, Makoda da Dambatta har yanzu ba su fara aiwatar da shirin ba bayan shekaru biyu da soma shi.

Wasu daga cikin jami’an da abin ya shafa a karamar hukumar Tsanyawa sun fadawa wakilinmu cewa, duk da cewa sun shafe sama da shekara guda suna ganin sakon banki daga Hukumar KPHCMB da KASHMA, amma ba za su iya fitar da kudaden ba saboda rashin littafin cakin kudi  daga bankunansu.

Asibitin Tsanyawa mai dauke da rajistar mutane  583  dake a karkashin shirin, Ko mutum daya  babu wanda ya amfana da shirin.

"Muna da sama da Naira  4-609-520 a asusun mu, sai dai kawai suna saka mana kudaden ne amma  ba za mu iya cirewa  ba saboda rashin cakin kudi  da zamu yi amfani dashi,  in ji shugaban Asibitin, Sharhabil Habeeb.

"Yawancin Mutanen dake karkashin shirin suna zuwa neman magani amma ba za mu iya yin komai ba, koyaushe muna rokonsu da su yi hakuri," A cewarsa.

Da aka tuntubi Babban Sakataren Hukumar Kula Da Asibitoci ta jihar Kano KPHCMB Dr. Tijjani Hussain, ya ce ba a fara aiwatar da shirin a kananan hukumomin shida ba saboda jinkirin bayar da litattafin Cakin Kudi , amma kuma yaki fadar sunayen bankunan.

Dr. Hussain ya ce bayan bin diddigin da aka yi na tsawon shekaru biyu, hukumar ta bukaci bankin ya mayar da dukkan kudaden shirin na  BHCPF da ke hannun ta, tare da gaggauta bude wani asusu a wani banki domin gudanar da shirin.

TAKUNKUMIN HUKUMAR KPHCMB YA KAWO TSAIKO WAJEN SAMUN WANI ABU DAGA  HUKUMAR BUNKASA  KIWON LAFIYA A MATAKIN FARKO  TA KASA A MAFI YAWA DAGA CIKIN ASIBITOCIN JIHAR KANO

Duk da cewa kudaden tafiyar da shrin ana tura su ne kai tsaye  ga Asibitoci  381 dake amfana da shirin  sai dai  takunkumin  da aka saka  daga  bangaren hukumar  Bunkasa lafiya a matakin farko  ta kasa  wanda ya shafi  kudaden tafiyar da ayyuka da  gyaran kayan aiki da biyan ungozoma da  daukar  sabbin ma’aikata  ya sa an dakatar da shirin  sama da  shekara guda a wasu asibitocin a nan  Kano.

An dakatar da gine-gine da gyare-gyaren da ake yi a Asibitin  Gungara da na Kademi da Garmarya da ke karamar hukumar Gaya,  bayan da aka yi zargin cewa an saka masu takunkumi.

AIKIN DA YA TSAYA CAK A ASIBITIN GUNGAYA

AIKIN ASIBITIN GARMAYA

AIKIN ASIBITIN GARMAYA

 

HUKUMAR  KPHCMB TA KARE MATAKIN SAKA  TAKUNKUMI, INDA TA YI ZARGIN YIN RUFA-RUFA WAJEN  AIWATAR DA SHIRIN

Ma’aikatan dake da ruwa da tsaki wajen aiwatar da shirin a matakin jiha sun musanta zargin cewa sun saka takunkumi wajen aiwatar da shirin domin wata bukata ta kashin kai.

Da yake mayar da martani  akan  tambayar da wakilinmu ya yi masa,  Dr. Tijjani Hussain, Babban Sakataren  Hukumar KPHCMB, ya ce matakin ya shafi  ma’aikatan wasu asibitoci ne kawai  saboda rashin yin komi a faiyace. “A wasu Asibitocin , wani shugaban asibiti  zai ciro kusan Naira miliyan biyu yayin da ka’idar ta ce ba za su iya fitar da sama da Naira Dubu 50 ba; wasu za su ce sun yiwa wasu dakunan asibiti fenti kuma ba a yi hakan ba.

Ya kara da cewa takunkumin ya kuma shafi biyan ma’aikatan  ungozoma da ma’aikatan wucin gadi dama daukar sabbin ma’aikata  saboda yadda ake tafka kura-kurai a harkar daukar ma’aikata da biyan albashi. Ya kuma ba da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba za a shawo kan dukkan kalubalen da aka gano.

Duk da haka, malam  Sani – direban dake tallafawa jama’a a  garin Jeli , ya baiyana  cewa motarsa ​​mai shekaru 15 ba za ta iya cigaba da kasancewa a yadda  take ba din-din din.

Sai dai ya yi fatan  cewar mutuwar Hassana zata kasance  ta karshe da za a iya samu daga  bangare mata masu dauke da juna biyu  dake  mutuwa  ba zato ba tsammani a garin , idan  har gwamnatin jiha ta samar da ingantaccen Asibiti  da isassun ma’aikata ga mazauna kauyen.

Wannan rahoton nA  Hadin gwiwa ne da Cibiyar bin didddigi kan  Kasafin Kudi  ta Duniya IBP da Cibiyar binciken ‘kwakwaf  da bayar da rahoto  ta Duniya, ICIR.

 

More from Labarai