On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Cutar Amai Da Gudawa Ta Halaka Mutane 80 A Wasu Jihohi 9 Na Najeriya

cutar amai da gudawa ta hallaka mutane 80 a fadin jihohi 9 dake fadin kasar nan a dai dai lokacin da adadin masu dauke da cutar ya karu zuwa dubu 4 da dari da hamsin da uku.

Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasa ita ce ta bayyana hakan ta cikin wani rahoto na makwanni 39 data yi wanda ta fitar da safiyar yau.

A cewar rahoton hukumar NCDC, kaso 86 na masu dauke da cutar sun zo ne daga jihohi 11, inda jihar Borno take kan gaba da mutane dubu 3 da dari 6 da 63, sai jihar Yobe dake biye mata baya inda take da mutane dubu 1 da dari 6 da 32.

Sauran jihohin sun hada da katsina wadda keda mutane dari 7 da sittin da 7, da kuma jihar Taraba dake da mutane dari 6 da saba’in da biyar, yayin da jihar Cross River take da mutane dari 6 da arba’in da tara, sai Gombe tana da mutane dari 4 da saba’in, da Jigawa akwai mutane dari 4 da sha bakwai da Bauchi dake da mutane dari 3 da hudu.