On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Da Yuyuwar Jami'oi Su Sake Shiga Yajin Aiki A 2024

ASUU

Da yuyuwar a sake fuskantar tafiya yajin aikin jami’oi a kasar nan a shekara mai zuwa, sakamakon kason da aka ware masu cikin kunshin kasafin kudin shekara mai zuwa bai taka kara ya karya ba, kamar yadda kungiyar malaman jami’oi ta kasa ta baiyana.

A hirarsa da manema labarai a jiya, Shugaban kungiyar na kasa, farfesa Emmanuel Oshodoke, Ya  ce  a yayin yakin neman zaben shugaban kasa Bola  Tinubu, ya yi alkawarin karawa kasafin fannin ilimi kimanin kaso 15 cikin 100.

Sai dai kuma y ace  kungiyar  ta baiyana mamakinta kan yadda aka warewa bangaren ilimi naira tiriliyan 2 da bilyan 18, wanda ya kama kaso 7 da digo 9 cikin 100  na kasafin kudin,  kuma hakan ya saba ta tanadin hukumar bunkasa ilimi da raya al’adu ta majalisar dinkin duniya UNESCO, wadda ta bukaci a rika warewa bangaren kaso  26 cikin 100.

Dagan an shugaban kungiyar malaman jami’oin ta kasa  ya shawarci gwamnati da  ta yi zama na musamman da  ‘yan majalisar zartawa domin karawa  fannin ilimi kaso mai  tsoka a cikin kasafin kudi.