On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Dakataccen Shugaban Hukumar EFCC Yana Tsare A Hannun DSS

A yanzu haka dakataccen shugaban Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Abdulrashid Bawa na tsare a hannun jami’an Hukumar tsaron farin kaya ta DSS.

Bawa  ya isa  shalkwatar  hukumar tsaron ne  da  karfe 9  da miniti  biyu na daren jiya, Kamar yadda mai magana da yawun hukumar  DSS,Peter Afunanya  ya  tabbatar  ta  cikin wata sanarwa.

Sanarwar  ta baiyana cewar  gaiyatar da hukumar tsaron farin kaya  ta DSS  ta yiwa  Abdulrashid Bawa nada nasaba  da binciken da ake gudanarwa a kansa.

A  jiya ne, Shugaban kasa,Ahmed Bola Tinubu ya dakatar da  shugaban hukumar  ta EFCC, bisa  zarginsa  da aikata wasu lefuka,wanda  daukar matakin zai bada damar  yi masa bincike.