On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

'Daliban Najeriya Na Rokon Mahukunta Su Gaggauta Dawo Da su Gida Daga Kasar Sudan

‘Daliban Najeriya da ke karatu a Sudan sun roki gwamnatin Najeriya da ta taimaka musu wajen kwashe su daga kasar cikin gaggawa.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da shugaba da sakataren kungiyar daliban Najeriya a Sudan suka sanyawa hannu.

A cikin wata sanarwar manema labarai da suka aikowa Arewa Radio a daren jiya, daliban da suka makale sun ce suna rayuwa cikin fargaba sakamakon rikicin da ya barke tsakanin sojojin Sudan da dakarun sa-kai.

A cewarsu, a cikin kwanaki ukun da suka gabata, a kusa da birnin Khartoum, babban birnin kasar, ana fama da harbe-harbe a kai a kai, da tashin bama-bamai da jiragen sama.