On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Dalibin Da Aisha Buhari Tasa Aka Kama Zai Iya Rasa Rubuta Jarabawarsa Ta Karshe

DALIBI AMINU DA AISHA BUHARI

Lauyan Dalibin nan dake jami’ar taraiyya ta garin Dutse a jihar Jigawa, mai suna Aminu Adamu, wanda aka kama bayan ya yi wani rubutu akan mai dakin shugaban kasa, Aisha Buhari, a shafinsa na twitter, Ya ce ya nemi a bada belin dalibin domin ya samu damar fara rubuta jarabawarsa ta karshe a jami’ar a ranar 5 ga watan da muka shiga na Disamba.

An kama Aminu Adamu ne bayan ya  rubuta cewar, Mama ta  ci tayi kiba  da kudin Talakawa, wanda ya wallafa rubutun a shafinsa na Twitter.

Lauyansa mai suna  CK Agu, ya  fadawa manema Labarai cewa  an gurfanar  da  wanda yake karewar ne a Abuja, kuma bai amsa cewar ya aikata lefin da ake tuhumarsa dashi ba, ya kara da cewa  tun a ranar   25 ga watan Nuwamba ne ya nemi a bada belin dalibin amma aka hana.

A cewarsa  Kotu  ta umarci jami’an yansanda  dasu gabatar  ta  takardar neman bada dalibin beli  wanda kuma shine zai sa kotun ta yi duba kan bukatar tasu a yau ko gobe, kuma tuni aka yi hakan.