On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

‘Dan Asalin Najeriya Anthony Joshua Ya Sha Kashi A Hannun Oleksandr Usyk Na Ukraine

‘Dan wasan kasar Ukraine Oleksandr Usyk ya doke Anthony Joshua dan asalin Najeriya a jiya inda hakan ya bashi damar cigaba da rike kambunsa na damben boksin na duniya a WBA, WBO, IBF da IBO a Jeddah.

Nasarar ta sa dan wasan mai shekaru 35 a duniya ya kai fafatawa 20 ba tare da an doke shi ba yayin da Joshua mai shekaru 32 ya yi rashin nasara ta  2 a rayuwarsa.

Ɗan damben boksin ɗan kasar Ukraine, ajin masu nauyi, Oleksandr Usyk, ya kare kambunsa daban-daban, bayan da ya yi nasara a kan ɗan Birtaniya, Anthony Joshua da yawan maki.

Sun yi fafatawar ce, wadda aka yi wa lakabi da Rage on the Red Sea, a birnin Jeddah na kasar Saudiyya ranar Asabar da daddare.

Alkalai biyu sun bai wa Usyk maki 115-113 da 116-112 , yayin da alkali na uku ya bai wa Joshua 115-113.

A watan Satumbar bara Usyk ya doke Joshua inda ya lashe kambu uku, daga baya ya shiga aikin sojan kundunbala, bayan da Rasha ta fara kai wa Ukraine hare-hare tun daga watan Fabrairu.

Mahukuntan Ukraine sun shawarce shi da ya koma fagen dambe domin ya ɗaga martabar kasar.

Bayan tashi daga wasan, Usyk ya sadaukar da nasarar da ya yi ga sojojin Ukraine daga tsakiyar filin dambe da aka kawata da launin tutar Ukraine mai launin ruwan ɗorawa da bula.