On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Dan Takarar Majalisar Wakilai A Wudil Da Garko A Jam'iyyar NNPP Ya Rasu

Marigayi Alhaji Kamilu Ado

Allah ya yiwa Dan takarar majalisar wakilai na kananan hukumomin Wudil da Garko a karkashin jam’iyyar NNPP, Alhaji Kamilu Ado rasuwa.

Marigayin ya kasance  tsohon  mataimakin  shugaban rundunar  tsaro  ta CIVIL DEFENCE  na kasa,  wanda  ya koma ga mahallici  bayan  ya  yi  fama da gajeruwar  jinya, kuma da safiyar yau ne ake saran  za’a yi  jana’izar  marigayin.

Da  fatan  Allah  ya  gafarta masa.