On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Dan Wasa Nyemar Na Shirin Barin Kungiyar PSG

Neymar

Ana danganta dan wasan Brazil Neymar da komawa kungiyar kwallon kafa ta Manchester city mai buga gasar zakarun Premier

A cewar wasu  rahotanni, yanzu haka mai  horasawa  Pep Guardiola ya tuntubi dan wasan mai shekaru 31 domin  sanin inda  ya dosa  a kasuwar musayar 'yan wasa mai zuwa.

Kwantiragin Neymar  da  kungiyar  Paris Saint-Germain zai kare ne  a shekarar  2027 amma ana rade-radin cewa zai iya canza sheka zuwa gasar Premier.

Kazalika wasu rahotannin  kuma  na  alakanta shi da Manchester United da Chelsea.   Yayin da  Ita ma Beyern Munich take  hakon  daukar  dan wasan  na Brazil.