On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Dan Wasa Raheem Sterling Ya Koma Kungiyar Kwallon Kafa Ta Chelsea

DAN WASA RAHIM

Dan wasa, Raheem Sterling ya koma gida, bayan da bar kungiyar kwallon kafa ta Manchester city zuwa kungiyar kwallon kafa ta Chelsea kan kwantiragin shekaru biyar.

Dan wasan na Ingila ya kawo karshen zamansa na shekaru bakwai a Manchester City yayin da ya koma  abokiyar  karawarsu a gasar Premier ta Ingila a jiya.

Kungiyar ta Chelsea ta  fitar da tsabar kudi har  fam miliyan 47 da Dubu Dari 5 domin siyan dan wasa Sterling, wanda ya lashe kofunan lig hudu a zaman da yayi a  Etihad.

Chelsea ta tabbatar da kulla   yarjejeniyar daga sansanin ta na daukar horo domin tunkarar  kakar wasa ta bana dake kasar  Amurka, inda ta kara da cewa Sterling a shirye yake ya fara aiki da kungiyar.