On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Dandazon Mata Magoya Bayan Jam’iyyar NNPP Sun Gudanar Da Zanga-Zanga

Magoya bayan NNPP

Magoya bayan jam’iyyar NNPP a  nan kano na cigaba da yin zanga-zanga  domin  kalubalantar hukuncin da kotun daukaka kara  ta yanke, na sauke gwamna Abba Kabir  Yusuf  na nan jihar Kano daga kan kujerarsa.

A wannan karon, Mata magoya  bayan jam’iyyar sun gudanar da tasu zanga-zangar a shalkwatar rundunar yasnandan  jihar na kano,  domin baiyana hukuncin da kotun daukaka karar ta yanke a matsayin rashin adalci.

Duk da cewar hukumomin yansanda sun hada gudanar da zanga-zangar, to sai dai  a jiya daruruwan mata sanye jajayen kaya dauke da kwalaye da aka yiwa rubutu daban daban, sun gudanar da tattakinsu tun daga gidan  sanata Rabiu musa kwankwaso zuwa shalkwatar rundunar yasnandan jihar kano.

Sun bukaci a yi  adalci  tare da  sake  jaddada cewar gwamna  Abba ne ya lashe  zbaen gwamnan jihar kano d aka yi  cikin watan maris din bana.

Nan ma a jiya ne, Wasu magoya bayan gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf, suka yi dandazo a harabar wasanni ta Lekan Salami dake birnin Badun a  jihar Oyo, domin gudanar da addu’o’i tare da gudanar da zanga-zangar lumana domin mika musu bukatunsu na ganin gwamna Abba ya ci gaba da mulkin kano.

Magoya bayan sun fito kan tituna dauke da alluna, da aka yiwa  rubuce-rubuce irin su, A yi Adalci  a Kano, Kano Abba aka  Zaba,  Abba ne zabin mu, da sauransu.

Sun gargadi bangaren shari’a kan duk wani abu da zai iya haddasa rikici a Kano da sauran sassan kasar nan.

Da yake zantawa da manema labarai a Badun,  mai baiwa gwamnan jihar Kano shawara na musamman kan harkokin kare namun daji, Ahmad Sawaba, ya yi kira ga kotun koli da ta duba hukuncin da kotunan baya suka yanke a  tsanake  sannan kuma  ta yi adalci.