On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Darajar Naira Ta 'Dan Farfado

Darajar Takardar Naira ta samu Armashi A ranar Talata Bayan da aka canzar da ita akan naira 420 da kobo 27 akan kowace Dala 1.

Hakan ya nuna cewar Takardar Naira ta samu ribar kaso Sifili da Digo 25 bisa  100, idan aka kwatanta da yadda aka canzar da ita a ranar  Litinin kan naira 421 da kobo 33.

An  fara  canzar da Takardar Naira ne akan farashin naira 420 da kobo 71 a ranar Talata, A yayin da mafi kololuwar farashin da aka siyar da ita ya kama naira 4,44, Sannan kuma farashi mafi sauki da aka canzar da ita ya kama naira 420 da kobo 27 a bisa farashi na Hukuma.

Gabaki daya anyi  Musayar kudadaden Dala har kimanin Dala Milyan 10 da 8 da Dubu  Dari  6 a ranar Talata.

 

 

More from Labarai