On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Dino Ya Zama 'Dan Takarar Gwamna Na Jam'iyyar PDP A Jihar Kogi

Sanata Dino Melaye ya zama dan takarar jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Kogi da za a yi ranar 11 ga watan Nuwamba na shekarar 2023.

Shugaban kwamitin zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP Sanata Ahmed Makarfi shine ya sanar da sakamakon zaben, inda ya ce Melaye ya samu kuri’u 313 wanda hakan ya bashi damar samun tikitin takarar.

Tsohon dan majalisar dai zai fafata da dan takarar jam’iyyar APC, Usman Ododo a zaben.

Kwanaki kadan gabanin  zaben na fidda gwani, Gwamna Nyesom Wike na Rivers ya bayyana Melaye a matsayin dan wasan barkwanci, yana mai cewa PDP zayi asara ne kawai  da ta hanyar mika tikitin ta ga tsohon dan majalisar ta tarayya.

Amma Melaye ya mayarwa Wike martani, yana mai cewa ya san yadda ake horar da zaki, yayinda   ya bayyana kalaman Wike a matsayin mara tushe.