On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Doguwa Da Wase Sun Ki Amincewa Da Tsarin 'Yan Takarar Shugabancin Majalisar Wakilai Na Masalaha

DOGUWA DA WASE

To sai dai da Alama matakin da uwar jam’iyyar APC ta dauka bai yiwa wasu daga cikin masu neman shugabancin majalisar dokokin ta kasa dadi ba, Inda suka nuna rashin amincewarsu da yin amfani da tsarin ‘yan takara na masalaha

A wani taron manema labarai da suka kirawo a daren jiya, Mataimakin kakakin majalisar  wakilai, Ahmed Idris Wase, Da shugaban masu rinjaye a zauren majalisar, Alhasan Ado Doguwa,Sunyi  fatali da tsarin ‘yan takarar  na masalaha,  wanda  uwar  jam’iyyar  APC  ta kasa ta sanar a ranar  Litinin.

Da suke jawabi a  wajen taron manema Labaran, Ahmed Wase da Alhasan Ado  Doguwa  sunce  ba zasu kyale  a yiwa  sabon zauren majalisar dokokin ta kasa  zagon kasa  ba.

Bugu da kari sun lashi  takobin cigaba da takararsu  ta neman kujerar  kakakin zauren majalisar wakilai ta kasa.