On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Doguwa Ya Janye Kudirinsa Na Zama Kakakin Majalisar Wakilai

DOGUWA

Shugaban masu rinjaye a zauren majalisar wakilai Alhasan Ado doguwa ya janye daga takarar kujerar kakakin majalisar wakilai ta kasa.

Doguwa  ya sanar da janyewar ne  a daren jiya, a yayin wani taro  da aka  shirya  tsakanin zababbun ‘yan majalisar  wakilai, a otal din Transcorp Hilton dake Abuja.

Ya  kara  da cewar ya  janye  daga takarar ne  tun daga ranar da  jam’iyyar APC  ta aiyana  Tajudden Abbas da Benjamin Kalu, a matsayin wadanda  zasu gaji buzun kakakin majalisar wakilai da kuma mataimaki.

Alhasan Ado Doguwa  ya baiyana cewar, Tajudden Abbas  ya cancanta  kuma yana  da gogewa  ta sanin yadda zai jagoranci majalisar.

Kazalika y ace  ya dauki matakin ne domin   nuna  goyon bayansa  ga zabin da jam’iyyar  ta yi,  kasancewar  shima  ya  amfana da tsarin nan  na shiyya-shiyya wajen raba mukamai.

 

More from Labarai