On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Dole Ne Mu Karfafa Tsarin Rigakafi A Najeriya - Dr Faisal Shu'aibu

Gwamnatin tarayya ta ce kaso 97 cikin 100 na mutanen da suka kamu da cutar mashako da akafisani da Diphtheria a Najeriya sun fito ne daga jihohi biyar na arewa.

Babban Daraktan Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta kasa, Dr Faisal Shuaib wanda ya bayyana haka a wata  ziyarar aiki  domin duba matakan da ake dauka na yaki da barkewar cutar mashako  a jihar Kano,  ya ce jihohin su ne Kano da Yobe da Borno da  Katsina da kuma Kaduna. 

Dr Faisal wanda ya ziyarci cibiyar kula da masu fama da  cutar mashako dake asibitin kwrarru na  Murtala Muhammed a Kano, ya ce bayanai sun nuna sama da kashi 80 cikin 100 na wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar da kuma wadanda suka mutu ba su yi  allurar rigakafi ba. .

Ya kara da cewa Najeriya na bukatar samun tsarin rigakafi na yau da kullum mai  inganci kuma akwai bukatar iyaye su kai rahoton duk wata daga ta cutar daga 'ya 'yansu zuwa kwararru domin daukar matakai.

Ya yi tsokaci kai tsaye kan labaran karya da game da alluran rigakafi, kamar yadda aka yada jita-jita akan cewa rigakafin  polio yana haifar da rashin haihuwa. 

Daga nan, Dokta Faisal Shuaibu ya bukaci ‘yan Najeriya da su hada kai da kafafen yada labarai domin yada sahihan bayanai dangane da rigakafi.