On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Dole Ne Tinubu Ya Aiyana Kadarorin Da Ya Mallaka Kafin Ranar 29 Ga Watan Mayu

Tinubu

Hukumar ‘Da’ar Ma’aikata ta kasa, Ta baiyana cewar ya zama wajibi, Zababben shugaban kasa Asiwaju Bola Tinubu Da mataimakinsa Kashim Shettima tare da gwamnoni 28 da aka zaba, su baiyana kadarorin da suka mallaka kafin ranar 29 ga watan Mayu da muke ciki.

Kazalika Sanatoci  da sauran zababbun  ‘yan majalisar wakilai  ta kasa  ana saran zasu baiyana dukiyar da suka mallaka kafin ranar 5  ga watan yunin bana,  Lokacin da zasu  sha  rantsuwar  kamar aiki.

Mai magana  da  yawun  hukumar,  Uwar gida  Veronica kato  ce  ta  tabbatar da haka  a  Abuja ,  Tana mai cewar  baiyana kadarorin  ya zama wajibi ga mutanen.

Ta kara da cewar  da dama daga cikin wadanda aka zaba  sun fara  karbar  Fom na  baiyana kadarorin da suka mallaka a  rassan ofishin hukumar  dake jihohin kasar  nan, kuma ana saran zasu mayar  dashi kafin  lokacin rantsar dasu.

More from Labarai