On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Dole sai anyi gyara a kasafin kudin 2022 - Buhari

A cikin wasikar, Shugaban Kasa  Buhari, Ya ce gyara

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar dattijai ta amince da karin kudin biyan tallafin Mai na shekarar 2022 da naira tiriliyan 3 da bilyan Dari 5 da 57, inda za'a samu Karin naira biliyan  Dari 4 da 42 da Dubu 72 Wanda zai kama zuwa naira tiriliyan 4.


Kazalika Majalisar dattawan ta kuma karbi takardar da shugaban kasar ya aike mata da ita, inda yake neman majalisar ta amince da Karin ciyo wani bashi  domin cike gibin   kasafin kudin  na shekarar 2022.

Bukatar Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 5 ga watan Afrilun da muke ciki, wadda shugaban majalisar dattawa, Sanata  Ahmad Lawan ya karanta ranar Talata  Yayin zaman majalisar.

A cikin wasikar, Shugaban Kasa  Buhari, Ya ce gyara ga tsarin kasafin kudi na shekarar 2022 ya zama wajibi bisa la’akari da sabbin ci gaba da aka samu ta bangaren  tattalin arziki na duniya da na Kuma na cikin gida.