On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Donald Trumph Ya Maka Tsohon Lauyansa kotu

TRUMPH

Tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya kai tsohon lauyansa kotu kan zarginsa da cin amanarsa dangane da wata kwangila ta dala miliyan 500 da suka kulla a tsakaninsu.

Ya ce lauyan mai suna  Michael Cohen ya saba ka’idojin aikinsa na  lauya wanda  ya  kamata  yayi amfani da kwarewarsa  wajen bashi kariya.

Shari'ar dai ta zo ne a daidai lokacin da abokan Trump ke  cigaba da  farwa  Lauya  Cohen, wanda shi ne babban  mai  gabatar da  shaida a binciken da ake yiwa  tsohon shugaban kasar  a wata  kotu dake  New York .

Idan ba’a manta ba a  makon da ya gabata wani mai gabatar da kara a  Manhattan ya tuhumi Mista Trump da  aikata lefin  zamba cikin aminci ta hanyar da bayar da wasu makudan kudi  ga wata jarumar fina-finan batsa.