On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Donald Trumph Zai Sake Gurfana Gaban Kotu A Yau

TRUMPH

A daren jiya ne Tsohon shugaban kasar Amurika Donald Trump ya isa birnin Miami na jihar Florida kwana daya kafin ya gurfana a gaban kotu a safiyar yau bisa zarginsa da karkatar da bayanan tsaron kasar.

Tsohon shugaban na Amurika ya taso ne daga  wajen  wasan  kwallon gora  da ke Bedminster, New Jersey, zuwa wurinsa  na  shakatawa  mai suna  Trump Doral da ke kusa da birnin na  Miami.

Mista Trump na fuskantar tuhume-tuhume da dama na rike bayanan sirri ba bisa ka'ida ba, Wannan dai shi ne karo na biyu a wannan shekara da ake tuhumarsa da aikata wani laifi.

Donald Trump, wanda ke yakin neman komawa fadar White House a shekarar 2024, ya musanta aikata ba daidai ba yayin da yake fuskantar tuhuma ta farko da gwamnatin kasar  ta taba yi wa wani  tsohon shugaban kasar  Amurika.