On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Donald Trumph Zai Sake Yin Takarar Shugabancin Kasar Amurika

Tsohon shugaban kasar Amurika Donald Trumph

Tsohon tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana kudirinsa na neman zama shugaban kasa a fadar mulki ta White House a shekarar 2024.

Tuni dai tsohon shugaban kasar, ya baiyana burinsa  na sake mulkar kasar Amurika a  shekarar 2024, inda  ya  kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa a hukumance, sannan kuma ya  mika takarda ga hukumar zabe  kasar dake  ayyana kansa a matsayin dan takarar shugaban kasa tare da kafa sabon kwamitin yakin neman zabe.

Wannan dai ya biyo bayan zaben tsakiyar wa’adi da aka gudanar a farkon wannan wata da ke nuna cewa ‘yan takarar da ya zaba,  sun sha kaye wanda hakan ya yi lahani ga  karfin da  jam’iyyarsa ke dashi.

A yau ne, ake  sa ran, Tsohon shugaban kasar Amurika Donald Trump zai yi jawabi a wani wurin shakatawarsa  dake jihar  Floridan Amurika.